Adam A Zango ya gwangwaje babban yaron sa da sabuwar mota

0
573

A safiyar yau darakta Saifullahi Safzor ya cika da murna, inda ya wallafa hoto da bidiyon mota kirar Peugeot 307 ana wanke ta a wajen wankin motoci, inda yake kalamai na godiya ga fitaccen jarumi Adam A Zango, a cewarsa Zango ne ya gwangwaje shi da ita.

Duk da yake dai ba wannan ne karo na farko da Zangon ke irin wannan kyauta ta bajintar ga yara da makusantan sa ba, amma jarumin na ta shan yabo da fatan alkhairi, inda shi kuma darakta Safzor ake yi masa murna gami da sam barka.

A kwanakin baya ma dai fitaccen mawakin nan na siyasa, wato Dauda Kahutu Rarara, ya gwangwaje mawakin nan na Kwankwasiyya Aminu Dumbulum da sabuwar mota da kuma kudi har naira miliyan daya.

Rarara dai ya yiwa wannan mawaki kyauta ne bayan fitar shi daga jam’iyyar ta PDP Kwankwasiyya ya dawo jam’iyyar APC.

Mawakin dai ya wallafa bidiyonsa da Rarara ne a lokacin da yake mika masa kyautar mukullin motar mai kirar Honda ‘Discussion Continue’ da kuma zunzurutun kudi har naira miliyan daya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here