Adam A Zango ya bayyana dalilin da yasa aka daina ganin shi a shafukan sadarwa

0
329

Duk wanda yake bibiyar jarumi Adam A Zango a shafukan sadarwa zai fahimci cewa kimanin mako biyu da suka wuce jarumin yayi batan dabo.

Sai dai sakamakon damuwar da masoyansa suka yi sunyi ta tambayar shi halin da yake ciki, inda a karshe jarumin yayi bidiyo ya bayyana musu halin da yake ciki.

Jarumin yayi magana ne cikin gurbataccen turancin nan da ake kira da turancin Legas ko kuma Pidgin English, inda yake cewa:

“Eh Sebzo ya kake? Na ji masoyana suna tambayar ina na shiga, wasu ma har suna tunanin ko bani da lafiya ko wani abu ya faru dani.

“Kai yafi dacewa ka gaya musu ina nan lafiya, babu abinda ya same ni, kawai naga ya kamata na dan samu hutu daga hawa yanar gizo, saboda naga wahalhalun kafafen sadarwa sun yi yawa, ko ina ka duba labarai ake yadawa na karya, ni kuma bana son ciwon damuwa ya kamani a wannan mulkin na Buhari.

“Yan uwa idan baku kula da kanku ba, babu wanda zai kula da ku, ku saurari shawarwari, amma shawarwarin wasu rufa-rufa ce.

“Samari matasa da ‘yan mata a mike mu nemi na kanmu mu daina zaman banza, mu daina dora laifi akan gwamnati koda yaushe, idan baka dage kayi aiki tukuru ba, babu wanda zai baka sisin kobo ba tare da ka roka ba.

“Saboda haka ku dage ku samu kudi, saboda kudi sune za su baka damar mallakar komai ba tare da ka roka ba, kun san ance roko yana zubar da mutunci, musamman ma idan ka roka aka hanaka.

“Saboda haka duk masu saurarona idan kana yi mini fatan alkhairi, nima ina yi maka fatan alkhairi, idan kuma kana yi mini fatan tsiya kai da Allah.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here