Abinda ke faruwa da Tinubu sakayya ce ta Allah, sai yayi aman duk abinda ya sata – Bode George

0
577

Jigo a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Olabode George, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, inda ya ce shine mutumin da ya kawo rikici a cikin jam’iyyar APC.

Bode George, wanda yake tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya caccaki Tinubu akan yadda ya tafiyar da mulkin jihar Legas, inda ya ce: “Lokacin tafiyar shi ya kusa, kuma sai yayi aman duka abubuwan da ya sata.”

Bode George dai ya bayyana hakane a lokacin da yake mayar da martani game da maganar da Tinubu yayi ranar Asabar, inda yayi watsi da zancen cewa zai fito takarar shugaban kasa a shekarar 2023, da kuma rikicin dake faruwa a jam’iyyar APC.

A cikin sanarwar Tinubu ya ce har yanzu bai gama yanke shawara game da fitowa takarar shugabancin kasa ba a shekarar 2023, inda yace abinda yasa a gaba yanzu shine ya taimakawa Najeriya ta fita daga matsalar tattalin arziki da take ciki sakamakon COVID-19.

Da yake magana a wata hira da yayi da The Independent, wacce suka wallafa a yau Litinin dinnan 29 ga watan Yuni, Cif Bode George ya ce:

“Tun a farko na sanar da su cewa jam’iyyar APC jam’iyya ce ta bakin ‘yan siyasa. Idan ka samu babbar jam’iyya irin wannan kuma wani yake kokarin ya kwace komai, dole za a samu matsala.

“Na farko dai abin kunya ne a tsarin shugabancin kasa, a ce wani wanda ba shi da kowanne mukami ya fito ya ce shine shugaban jam’iyya na kasa.

“Daga yaya haka zai yiwu? Shugaban jam’iyya daya ne kawai, shine shugaban kasa. Daga yaya wani can zai zo daga wani wuri ya ce shine shugaban jam’iyya ba shugaban kasa ba? Mai hakan yake nufi?

“Mun ga yadda aka cire Cif John Odigie Oyegun a matsayin shugaban jam’iyya. A gani na abinda yake faruwa da Tinubu sakayyace ta Allah. Kana ganin zaka iya debe duka dukiyar Najeriya ka tarawa danginka kamar yadda yayi a jihar Legas?

“Ba zai taba yiwuwa ba! Na tabbata sakayya Allah ce take kama Tinubu. Mun gargade shi a baya, amma yaki sauraron mu.

“Tinubu yana tunanin yafi kowa wayo ne.Yana tunanin zai iya kwace komai da komai, amma sun kwace masa komai da komai.

Da yake magana akan maganganun dake yawo dake nuni da cewa wasu na hannun daman Tinubu sun bukace shi da ya fita daga jam’iyyar APC, Cif Bode George ya ce:

“Wannan ya rage nashi, ba zan iya gaya masa abinda zai yi ba. Kwanan nan ya fitar da sanarwar cewa bai gayawa kowa yana son fitowa takarar shugaban kasa ba a 2023, kuma abinda yasa a gaba shine kawo gyara a Najeriya. Amma kuma zaku ga abinda yake yi a Legas. Mai zaku ce game da Alpha Beta? Wane yake karbar kudin Alpha Beta?

“Duk da haka yana cewa yana so ya kawo karshen wahalar da ‘yan Najeriya ke sha? Ya fara fito mana da duka kudin mu na Alpha Beta tun daga shekarar 2000 zuwa yanzu. Manajan daraktan wajen da ya gudu ya ce suna bin shi naira biliyan arba’in.

“Iya wannan kudin kawai zai iya taimakawa wajen fito da miliyoyin mutane daga talauci a jihar Legas a yau.

“Na sha cewa Tinubu sai yayi aman duka abubuwan da ya sata, kuma gashi lokacin ya zo.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here