Abin yana damuna idan naga matasan Afrika suna kwaikwayon Turawa – Jacob Zuma

0
399

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, ya nuna rashin jin dadinshi akan yadda ya ga matasa bakar fata masu ilimi suna kwaikwayon Turawa.

A wani dan gajeren bidiyo da ‘yar shi Dudu Zuma-Sambudla ta wallafa a shafinta na Twitter, tsohon shugaban kasar wanda ake tuhumarsa da cin hanci, an nuno shi zaune yana bayani.

Jacob wanda yayi magana da Turanci da kuma yaren Zulu, yayi magana da matasa na mahaifarsa ta Kwazulu-Natal, inda ya ce:

“Abinda yafi damuna shine kaga dan Afrika mai ilimi wanda yake likita ko kuma farfesa yana tunani irin na Turawa. Wannan ita ce matsalar da ke damuna, ba wai suna da tunani irin na Turawa bane kawai, sun mayar da Turawan abubuwan kwaikwayo…Wannan yana ci mini tuwo a kwarya.”

Wannan bidiyo dai wani bangare ne na hira da aka yi da shi, inda ya ce za a saki hirar tashi ga matasan Afrika a ranar Talata.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here