Yayin da aure yake wahala a wannan zamani, musamman wannan lokaci da mata suke neman ninka maza a yawa. Hakan bai hana wasu da yawa samun abokanan aure ba, musamman wadanda basu dauki rayuwar da zafi ba.

Duk da dai kowa yasan cewa aure lokaci ne na Allah dabarar mutum baza ta saka yayi ba, amma da yawa suna dorawa kansu karya da son abin duniya da ya sanya auren baya yiwuwa.

Wata tsaleliyar budurwa da ta wallafa hotunanta da wani saurayi a shafinta na Twitter ta bayyana yadda soyayyarsu ta samo asali har ya zuwa auren da suka yi.

Budurwar mai suna Ummeeta Rabiu, wacce alamu ke nuni da cewa sun shekara da aure, ta wallafa hotunan a shafinta inda ta ce: “Har yanzu ina mamaki haduwa a Twitter ne ya kawo mu wannan matsayi. Dama na sha fada cewa mu gwada mu gani. Da yanzu ba zan same ka ba. Ina matukar godiya ga Allah da irin rayuwar da muke yi tare. Alhamdulillah, ina sonka yanzu da har abada.”

Wannan rubutu da Ummeeta ta wallafa ya bawa mutane da dama sha’awa, inda wasu suke cewa irin wannan kyakkyawar budurwa bata nuna girman kai ba wajen yiwa saurayi magana a shafukan sadarwa, amma sai kaga wata can da ba kyau ne da ita ba ta dauki girman kan duniya ta dorawa kanta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here