Abin sha’awa: Hotuna yadda Uwa da ‘Ya da suka fara karatun jami’a a fannin lafiya a tare suka kammala a tare

0
105

Wata mata ‘yar kasar Ghana mai suna Cynthia Kudji, da diyarta sun kammala karatun jami’a a fannin lafiya daga makaranta daya.

A rahoton da cibiyar ma’aikatan lafiya ta kasar Ghana suka wallafa a shafinsu na Facebook, sun bayyana cewa wannan shine karo na farko da aka samu uwa da ‘yarta sun halarci makaranta a fannin lafiya a tare.

Dr. Cynthia Kudji ta fara aiki a fannin lafiya ne sannu a hankali, inda har ta kai babban matsayi a yankin Louisiana da Alabama.

Amma dawowarta mahaifarta kasar Ghana ya tabbatar da soyayyarta ta zama ma’aikaciyar lafiya.

A yanzu haka uwa da ‘yar sun kammala karatunsu baki days, inda suka zama manyan likitoci.

Yanzu haka ana shirin basu takardar zama ‘yan kasa a birnin New Orleans dake kasar Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here