A sanar damu idan za’a barmu mu halarci Sallar Idi a jam’i tun yanzu – Malaman jihar Kano sun sako Ganduje a gaba

1
474

A yayin da dokar hana zirga-zirga ta cigaba da aiki a jihar Kano sanadiyyar annobar coronavirus da ta addabi jihar, kungiyar malaman jihar ta bukaci ta san halin da ake ciki akan ko gwamnatin jihar za ta bari a gabatar da sallar idi a jam’i ko baza ta bari ba a karshen wannan wata na Ramadana.

Idan ba a manta ba gwamnati ta hana gabatar da taron jama’a ciki kuwa hadda sallar Juma’a da kuma zuwa coci, ta kuma hana zuwa kasuwanni da wuraren aiki da makarantu, duka a kokarin da take na rage yaduwar cutar Coronavirus.

Shugaban majalisar malaman na jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bukaci gwamnati ta sanar da su shin zai yiwu a gabatar da sallar idi din ko kuma babu dama, inda yace mutane suna tambayarsu akan yiwuwar hakan.

Sheikh Khalil ya ce da yawa daga cikin manyan malaman basu ji dadi ba akan hukuncin gwamnatin na kyale wasu ‘yan kasuwa su bude wuraren kasuwancinsu a wannan lokaci daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma, inda suke ganin in dai har za a bar mutane suje kasuwa wane irin dalili ne zai sa a hana zuwa masallaci ranar Juma’a.

Haka kuma yayi kira da a gabatar kwakkwaran bincike akan annobar da ta saka mutane ke mutuwa a jihar babu gaira babu dalili.

A cewar shi: “Muna kira ga gwamnati ta gabatar da kwakkwaran bincike akan dalilin da ya sanya mutane ke mutuwa a jihar nan babu gaira babu dalili, sannan kuma ta nemi hanyar kawo karshen lamarin cikin gaggawa.

“Haka kuma gwamnati tayi duba da cire dokar hana zirga-zirga, ta ware kasuwanni da shaguna da mutane zasu dinga zuwa suna siyayya dan rage cunkoson jama’a da kuma dakile yaduwar cutar.

“Mun ga yadda mutane suke fita bayan cire dokar hana zirga-zirgar, inda suke tinkarar cutar gadan-gadan ba tare da kokarin kare kansu ba.

“Muna so gwamnati ta sanya malaman addini, ‘yan kasuwa da sauran masu fada aji wajen neman mafita akan wannan lamari, da kuma karfafa tattalin arzikin jihar.

“Haka kuma muna so gwamnati ta fito ta yiwa mutane bayani akan yiwuwar sallar idi a karshen watan, idan zai yiwu ko kuma ba zai yiwu ba, saboda mutane na ta faman tambayar mu akan hakan.

“Sanin hakan zai taimaka mana wajen basu amsar tambayar da suke yi mana,” cewar Sheikh Ibrahim Khalil.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here