A kowacce rana muna kashe N4,500 akan kowanne mai cutar coronavirus a matsayin kudin abinci a jihar Bauchi

0
429

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce tana kashe naira 4,500 akan kowanne mutum daya mai dauke da cutar Coronavirus a matsayin kudin abinci kawai.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, (NAN) ya ruwaito, shugaban hukumar lafiya ta jihar, Rilwanu Mohammed, shine ya bayyana haka bayan wata hira da yayi da NAN.

Ya ce gwamnan jihar Bala Mohammed, ya sanya hannu akan kudin domin tabbatar da duk wanda yake da cutar ya samu isasshiyar kulawa.

Rilwanu ya bayyana cewa gwamnan ya bukaci wanda ya wakilta akan wannan aiki su tabbatar da kowa ya samu kulawar da ta kamata.

Rilwanu Mohammed
Hoto: NAN

“Gwamna ne ya umarce mu da mu kashe naira 1,500 a duk lokacin da za su ci abin akan kowanne mutum daya,” ya ce.

“Hakan na nufin 1,500 ta abincin karyawa, haka abincin rana dana dare suma 1,500, saboda baya so marasa lafiyan su sha wahala har aje ana yin zanga-zanga kamar yadda ya faru a wasu jihohin.

“Hakan ya mayar da kudin da ake kashewa akan kowanne mutum daya a rana zuwa N4,500.”

Rilwanu ya ce wani ya kira shi a waya wanda ya nemi a killace shi saboda wannan kulawa da marasa lafiyan suke samu a jihar.

Ya bukaci mutane suyi kokari su dinga bin dokar da hukumomin lafiya suka sanya domin rage yaduwar cutar a cikin al’umma.

“Mutane uku sun kirani sun nemi suma a killace su saboda irin kulawar da marasa lafiya suke samu a jihar nan.

“Daya daga cikin su dan karamar hukumar Giade ne, kuma saboda mun sallami mutane da yawa daga wannan karamar hukumar, akwai alamar ya samu labarin yadda muka basu kulawa shi yasa ya kira.

“Duka mutanen sun kirani suna hadani da Allah da annabi akan naje na dauko su na kai su wajen killacewa, sun ce suna so su ci kaji da kwai da ake bayarwa ga marasa lafiyan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here