A karshe dai masana a Najeriya sun gano maganin cutar Coronavirus

0
796

Masanan jami’o’in Najeriya sun gano maganin cutar coronavirus.

Masanan sun bayyana hakane a ranar Juma’ar da ta gabata 19 ga watan Yuni, inda suka ce sun samar da maganin ne a Afrika kuma ga ‘yan Afrika, amma zai yi aiki a wasu sassa na duniya idan an fitar dashi, The Guardian ta ruwaito.

Press Lives ta gano cewa shugaban kungiyar masanan Dr Oladipo Kolawole, ya ce za a dauki watanni 18 kafin a fitar da maganin ga jama’a.

Ya ce hakan ya biyo bayan bincike, nazari da kuma neman amincewar hukumomi kan amfani da maganin.

Kolawole ya ce nazarin da suka yi wanda ya basu damar samar da wannan magani, sun kashe kimanin naira miliyan bakwai da digo takwas (N7.8m).

A wani rahoton makamancin haka kuma, wata kungiyar masu bin addinin Katolika na Najeriya sun sanar da samar da maganin cutar na COVID-19, wanda suka kira shi da suna ‘Pax CVD Plus’.

Wata sanarwa da ta fito dauke da sa hannun shugaban su Anselm Adodo OSB, a ranar Laraba 29 ga watan Afrilu, ita ce ta bayyana haka. Shugaban ya ce maganin an samar da shi ne domin warkar da cutar Coronavirus.

Anselm ya ce maganin da suka samar da shi daga itatuwa, shine abinda yafi da cewa saboda yana da saukin hadawa, ajiyewa da kuma rabawa, sannan kuma duka masana lafiya da wadanda ba masana ba za su iya amfani da maganin saboda bashi da wata illa sosai.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here