A karshe dai gwamnatin tarayya ta cire dokar hana zuwa Masallaci da Coci

0
337

A jiya Litinin ne 1 ga watan Mayu gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa ta cire dokar hana zuwa wuraren ibada a fadin kasar.

Shugaban kwamitin gudanarwa kan cutar COVID-19, kuma sakatare na gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya ba da wannan sanarwar a yayin taron yau da kullum da kwamitin ta saba gudanarwa akan cutar.

Mustapha ya ce cire dokar hana zuwa wuraren ibadar ya dogara akan ka’idojin da PTF suka gindaya da kuma ka’idojin da gwamnatocin jihohi suka amince a kai. Sai dai kuma yace, gwamnati bata amince da tara mutane sama da 20 a wajen da bana ibada ko aiki ba.

KU KARANTA: Yunwa na neman yi mana illa saboda rashin kasuwa a wannan lokaci – Karuwai sun koka akan rashin ciniki lokacin Korona

Ya ce:

“PTF ta gabatar da abubuwan da take ganin sun kamata, kuma shugaban kasa ya sanya hannu akan hakan na nan da makonni hudu masu zuwa, inda dokar za ta fara aiki daga yau 2 ga watan Yuni zuwa 29 ga watan Yunin shekarar 2020.

“Gabatar da taron karawa juna sani a jihohi da kananan hukumomi dan wayar da kan jama’a akan cutar COVID-19, sannan kuma a yiwa mutane gargadi akan amfani da maganin da bai kamata ba; cikin abubuwan da za a nusar da jama’a shine hana taron da ya wuce mutane 20 in dai ba a wajen aiki bane.

“Cire dokar hana zuwa wuraren ibada bisa ka’idojin PTF da ka’idojin da gwamnatocin jihohi suka amince a kansu.”

Hakanan an sake daga dokar hana fita a kasar daga karfe 10 na dare zuwa karfe 4 safe, Wuraren sayar da abinci za su cigaba da rufewa, in dai ba wadanda za a siya a tafi daga wajen ba.

Makarantu, mashaya, wuraren motsa jiki, silima, wuraren shakatawa duka za su cigaba da zama a kulle har sai baba ta gani. Haka kuma mun gano cewa ma’aikatar sufurin jiragen sama na neman fara aiwatar da jigilar fasinjoji na cikin gida daga ranar 21 ga watan Yuni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here