A karshe dai Ganduje ya hana Almajiranci a jihar Kano baki daya

0
584

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya kawo karshen almajiranci a jihar Kano baki daya.

Ganduje, wanda yake magana da manema labarai a jihar game da cutar COVID-19 a jiya Laraba, ya bayyana cewa tsarin almajiranci a jihar ya zo karshe baki daya.

Gwamnan ya bayyana cewa idan har za a cigaba da almajiranci a jihar Kano to dole ne abi wasu ka’idoji don cigaba da tsarin a jihar.

Ka’idojin a cewar gwamnan jihar sun hada da sanya tsarin karatun boko a cikin, sannan kuma dole a samawa almajiran wuraren kwana, abinci, kayan sawa da dai sauran abubuwan da kowanne mutum yake bukata na yau da kullum.

Haka kuma Ganduje ya ce idan har tsarin almajirancin zai cigaba, dole ne a samawar da almajiran Malamai da suka cancanta, inda gwamnati za ta zabe su da kanta ta hanyar yi musu jarrabawa.

“Idan har aka bi wadannan dokoki kamar yadda muka lissafo su, zamu bari a cigaba da almajiranci a jihar Kano,” cewar Ganduje.

Banda gwamnan na jihar Kano, tuni gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa babu wanda zai kara yin almajiranci a jihar sa, inda har ya bayyana cewa matukar ya kama iyaye sun kai ‘ya’yansu almajiranci zai tunkuda su da Malaman zuwa gidan yari ko kuma ya ci tarar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here