A karon farko za’a sayar da Kauye dungurungum a kasar Sweden kan kudi Naira biliyan 2.7 saboda Korona

0
455

Wani kauye na kasar Sweden dake Sala an sanya shi a kasuwa, inda za a sayar da shi dala miliyan bakwai da digo biyu ($7.2m) kimanin naira biliyan biyu da digo bakwai kenan (N2.7b) a kudin Najeriya.

Kauyen baki daya yana da girman kadada 62 kuma yana dauke da gidaje 70 baki daya a ciki.

Gidaje a kauyen basu da wuraren dafa abinci, inda aka tsara bayar da abinci kullum a tsakiyar garin don tabbatar da adalci ga mazauna kauyen, kamar dai yadda New York Times ta ruwaito.

Wasu daga cikin gine-ginen kauyen sun shafe shekaru daruruwa, saboda kauye ne mai dumbin tarihi.

Yadda yanayin kauyen yake. Hoto: New York Times

Mutane 15 ne dai suka mallaki wannan kauye tun a shekarar 2002. Ana gabatar da bukunkuna na al’ada da dama a cikin kauyen.

Daya daga cikin mazauna kauyen mai suna Mats Wikman ya ce yawancin mutanen kauyen sun fara tsufa, kuma suna bukatar karin mutane.

An bayyana cewa daga cikin kauyukan dake kasar ta Sweden wannan kauye yana daya daga cikin wadanda ya samu kawowa wannan lokaci ba tare da abubuwan dake cikin shi sun lalace ba.

Kamar yadda hotuna suka nuna a tsakiyar garin akwai wani gini babba da mutanen kauyen suke amfani dashi a matsayin wajen yin bayan gida da kuma wajen tattaunawa.

“Babban kalubalen shine, zabar gidan da wanda ya sayi kauyen zai fara aiki a kanshi,” cewar Mr. Martinsson, daya daga cikin mazauna kauyen.

Wasu daga cikin abubuwan ban sha’awa dake cikin kauyen sun hada da tsohuwar coci da aka gina ta tun a karni na 19, da kuma wasu shaguna masu ban sha’awa.

Wani abin duba game da wannan kauyen, a lokacin da cutar Coronavirus ta bulla a kasar, kasar ta Sweden ba ta sanya dokar ta hana fita ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here