A karon farko yaya da kanwa da suke uwa daya uba daya za suyi aure

2
11640

Wasu yaya da kanwa da suke zaune a birnin New Jersey na kasar Amurka sun samu nasara a kotu bayan shafe shekaru goma suna bukatar kotun ta basu damar aurar junansu.

Kotun wacce alkalai guda biyar suke jagoranta ta amince da bukatar ta James Banes mai shekaru 41 da kanwarsa Victoria Banes mai shekaru 38, bayan shafe shekaru goma suna fama.

‘Yan uwan sun bayyana cewa sun jajirce akan wannan bukata tasu ne saboda miliyoyin ‘yan kasar Amurka da suke so suyi irin wannan aure amma suke tsoron fitowa su bayyana.

“Ana yin irin wannan auren tun a farkon duniya. Inda Adam da Hauwa’u basu yi ba da babu wanda zai kasance a duniyar nan yanzu,” inji James Banes a lokacin da yake bayyanawa manema labarai bayan nasarar da ya samu.

Juliane Grey, Lauyar James da Victoria Photo Source: World News Daily Report

“Daga yaya doka ta bani damar kwanciya da kowacce mace amma banda kanwata? Hakan ba abu ne da hankali zai dauka ba,” cewar James Banes.

‘Yan uwan da suka kusan shafe shekaru 15 a gidan yari sun bayyana cewa yanzu a shirye suke su fara tara iyali, musamman ma yanzu da suka samu ‘yanci.

“Babban burin mu dama shine mu samu zuri’a mai yawa, yanzu kuma mafarkin mu zai zama gaskiya,” cewar Victoria Banes, wacce ta ke gayawa manema labarai cewa cike ne da ita kuma tana sa ran haifar ‘yan biyu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

2 COMMENTS

  1. Subhanallah, wannan maganar babu dadinji, A wace aya yasamu a Bible akace masa Nanah Hauwa’u da Annabi Adamu uwarsu daya ubansu daya?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here