A karon farko Tinubu yayi magana akan zaben shugaba Buhari

0
3829

Sakamakon zargin da ake yi na cewa shi ya biya kudin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bola Tinubu ya karyata wannan magana.

Jigo a babbar jam’iyyar mai ci ta APC, ya ce bai kashe naira biliyan 35 ba a zaben 2015 da 2019 da aka gabatar ba kamar yadda ake zargi.

A yadda rahoto ya bayyana, Tinubu ya bayyana hakane a lokacin da yake hira da Bisi Akande, tsohon shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya.

Haka kuma yayi magana akan jita-jitar da ake yadawa ta cewa ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci amanarshi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Sai dai kuma a wata sanarwa da mai magana da yawun bakin Tinubu, Tunde Rahman ya fitar, Tinubu ya karyata wannan maganganu.

“Marubutan rahoton sun zargi cewa Asiwaju yayi wannan zargi ne a lokacin da yake tattaunawa da tsohon shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya, Cif Bisi Akande,” inji sanarwar.

“Da farko dai ba wai mutum daya ne ya zabi Buhari ba, al’ummar Najeriya ne suka zabe shi. Asiwaju Tinubu, ba zai yi alfahari akan matanak da mutane suke dauka. Hakanan, wannan zargi da ake yi tunani ne irin na marubutan wannan labari.

“Tinubu shine jigo a zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari na shekarar 2015 da kuma zaben shi da aka sake yi a shekarar 2019, tare da sauran shugabannin siyasa, da kuma ‘yan jam’iyyar APC da kuma ‘yan Najeriya baki daya.

“Ba shi da wani dalili da zai saka yayi dana sanin abinda yayi, ko kuma ya nuna rashin godiyarsa ga shugaba Buhari. Yana nan daram tare shugaban kasar da kuma manufofin gwamnatinsa kamar yadda ya saba.

“Babu wani abu da ya faru da ya saka ya canja zuciyrsa.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here