A karon farko an zabi mata-maza a matsayin magajin gari a kasar Faransa

0
229

Mairie Cau ta bar tarihi a matsayin mata-maza ta farko da aka zaba a matsayin magajin gari a kasar Faransa.

Matar wacce take ‘yar kasuwa ce da kuma ilimi a fannin noma an zabe ta a matsayin magajin gari a yankin arewa maso gabashin kasar Faransa a ranar 23 ga watan Mayu.

Da take tsokaci game samun nasarar lashe zaben na ta, Ms Cau ta ce ita ba mai fafutuka ba ce, amma kawai tana son ta mayar da hankali kan siyasa a birnin su.

Marie Cau mai shekaru 55 a duniya ta bayyana cewa: “Mutane basu zabe ni ba saboda ni mata-maza ce ko kuma ba mata-maza ba. Sun zabi cigaba da kuma cancanta ne. Mutane na bukatar canji.

“Ina da takarda wacce babu komai a cikinta, babu kasafin kudi, makarantu a rufe da kuma mutane da suke ta fama da cutar coronavirus.”

Ta samu tarba ta musamman daga wajen ministar kasa Faransa mai fafutukar kawo daidaito tsakanin maza da mata, Mariene Schiappa, wacce ta wallafa rubutu a shafinta na Twitter kamar haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here