A karon farko an haifi jaririya da iyayenta suka sanya mata sunaye guda 10

0
688

Wasu ma’aurata daga yankin kudu maso yammacin Najeriya sun zama abin kwatance a shafukan sadarwa bayan sun sanyawa jaririyar da suka haifa sunaye guda goma a lokaci daya.

Mijin mai suna Abdulakeem Badmus da matarshi mai suna Mariam Badmus, wadanda duka Musulmai ne, sun bar abin magana a shafukan sadarwar bayan sanyawa jaririyar ta su wadannan sunaye guda goma rigis.

Mata da miji da jaririyarsu mai suna guda goma Photo Source: @MrsRubeey Twitter Page

Kamar dai yadda aka sani wannan shine karo na farko da haka ta fara faruwa, domin babu wanda ya taba sanyawa dan shi suna sama da guda biyu ko bakwai, musamman ma a kabilar Yarabawa.

A lokacin da suke wallafa hotunan su dana jaririyar ta su a shafukan sadarwa, mahaifiyar yarinyar ta lissafo sunayen ‘yar ta su a kasa kamar haka:

KU KARANTA: Miji ya rasa yadda zai yi da ransa bayan ya gano tagwayen da matarsa ta haifa masa daya ba nashi bane

  1. Faheemah
  2. Adunola
  3. Ayodeji
  4. Abeni
  5. Mofolarayo
  6. Opemipo
  7. Abiodun
  8. Fiyinfoluwa
  9. Folashade
  10. Abiola
Source: @MrsRubeey Twitter Page

A wani rahoto kuma daga kasar China, wani magidanci ne ya rasa abinda ke yi masa dadi a duniya bayan ya gano wani sirri mai daure kan mai tunani.

Mijin dai ya gano cewa tagwaye guda biyu da matarsa da yake so fiye da komai a duniya ta haifa masa daya daga ciki ba nashi bane.

Hakan ya biyo bayan gwajin DNA da aka gabatar a asibiti bayan an dauki samfurin jini da gashin jariran.

Likitoci sun bayyana cewa ba kasafai aka fiya samun irin wannan lamarin ba, domin kuwa sai matar ta kwanta da maza biyu a kusan lokaci daya sannan hakan zai faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here