A karon farko an bude coci domin Musulmai su shiga suyi sallar Juma’a a kasar Jamus

0
315

Wata coci a birnin Berlin na kasar Jamus ta bawa Musulman da basu da wurin zuwa suyi sallar Juma’a damar shiga suyi sallah a ciki, bayan an sanya dokar hana sallah a jam’i a kasar.

An dakatar da ibada a jam’i ga al’umma a kasar ta Jamus a watan Maris a kokarin hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar. A yanzu haka an cire dokar taron jama,a inda ake barin mutane 50 kawai su taru a lokaci daya.

Masallacin Dar Assalam dake Neukolln yana daukar kimanin mutane 1,000, amma sanadiyyar dokar iya mutane kalilan ne kawai za su samu damar halartar sallah a jam’i. Cocin Martha Evangelical ba ta da nisa da Masallacin, inda shugabannin cocin suka fito domin su taimaka.

An gabatar da sallar Juma’a sau biyu a cikin cocin, daya da yaren Jamus, daya kuma da Larabci, inda masallata suka yi kokarin bin dokar kusantar juna, sannan suka sanya takunkumi.

“Wannan abu ne mai kyau. Mun gode kwarai da gaske, wannan hanya ce ta hadin kan addinai, kuma yana da kyau da coci tayi haka,” cewar mai magana da yawun masallacin Juanita Villamor, ya sanar da Newsweek.

“Wannan babban taimako ne a garemu, domin a yanzu muna da masu wa’azi guda biyu daya a masallaci daya a coci a ranar Juma’a, saboda haka mutane da yawa za su samu dama. Idan bamu samu cocin ba mutane da yawa baza su iya zuwa sallar Juma’a ba. Wannan yana da kyau kwarai da gaske.”

Monika Mathias, wacce take firist ce a cocin Martha, ta bayyana dalilin da ya sa cocin ta taimaka, ta gayawa Deutsche Welle: “muna ganin Ramadan a matsayin wata mai matukar muhimmanci, muna ganin addu’a da kuma kula da junanmu yana taimakawa al’umma wajen samun zaman lafiya.”

Haka shi ma limamin Masallacin Dar Assalam, Mohamed Taha Sabry, ya yabawa cocin akan abinda tayi, inda ya bayyana cewa: “Babban cigaba ne kuma muna yi musu godiya akan haka.”

A watan da ya gabata Sabry yayi gargadin cewa Masallatai da yawa za su shiga matsalar rashin kudi saboda kulle su da aka yi saboda Coronavirus, musamman a watan Ramadana da ba a samun taimakon Masallaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here