A karon farko Aku za ta zama shaida a kotu bayan wasu mutane sun yiwa wata mata fyade sun kashe ta akan idon ta

0
896

A cikin watan Disambar shekarar 2018 ne aka yiwa wata mata ‘yar kasar Argentina mai suna Elizabeth Toledo fyade a cikin birnin San Fernando.

An samu gawarta tsirara akan gado a cikin gidanta dake Buenos Aires, kusa da akun ta.

A yayin tattara bayanai akan wannan kisa nata a makon da ya gabata, ‘yan sanda sun dauki wani rahoto daga wajen daya daga cikin ‘yan sanda da ya ce ya jiyo Akun jim kadan bayan aikata kisan tana cewa, ‘no, Por favour, soltame!’ ma’ana “Ku bari, dan Allah ku kyaleni,” cewar rahoton.

‘Yan sandan sun yadda cewa Akun ta cigaba da maimaita kalaman karshe na uwargidan ta, a lokacin da mutane biyu suka yi mata fyade suka kashe ta.

Mai gadin wajen ya jiyo ihun mace a ciki. Sai ya garzaya domin yaga abinda ke faruwa, kawai sai yaga gawar Toledo tsirara akan gado, tare da Akun ta a gefe a cikin keji.

Haka kuma mutumin ya bayyana cewa ya jiyo lokacin da Akun take cewa ‘por que me pegaste?’ ma’ana “mai yasa kuke duka na?” a lokacin da daya daga cikin mutanen ya daki Toledo.

Yanzu haka dai an kama Miguel Saturnino mai shekaru 51 da kuma Jorge Raul Alvarez mai shekaru 62 da laifin kashe Elizabeth Toledo a Buenos Aires a shekarar 2018.

Lauya mai gabatar da kara Bibiana Santella, ta sanya maganar wannan Aku a cikin jerin shaidun da za a gabatar a gaban kotu, sauran shaidu sun hada da cizo da aka yiwa matar a hannunta, wanda aka bayyana cewa yayi daidai da hakorin daya daga cikin wadanda ake zargi.

Haka kuma binciken da aka gabatar a gidan matar an gano DNA na Alvarez, inda ya sanya ake zarginsu da wannan aika-aika.

Binciken asibiti ya nuna cewa sun yiwa matar fyade, sun mata duka sannan kuma suka kasheta.

Ms Toledo ta karbi hayar daki a gida daya tare da Miguel Saturnino Rolon da kuma Jorge Raul Alvarez a matsayin makwabtan ta.

Mutum na uku dake gidan shima an kama shi, amma baya gidan a lokacin da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here