A halattawa mata rike bindiga da barkonon tsohuwa kawai – Sarkin Gargajiya ya shawarci Buhari akan fyade

0
665

Sarkin Iwoland, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya shawarci gwamnatin tarayya ta halartawa mata amfani da bindiga da barkonon tsohuwa domin kare kansu daga masu fyade.

Sarkin ya bayyana hakane ta bakin sakatarensa na yada labarai, Alli Ibraheem, ya bukaci gwamnatin ta duba wasu hanyoyi na kawo karshen fyaden baya ga hukunta masu laifin idan an kama su.

Ya ce: “Yawaitar fyade da ake samu yayi yawa hakan yasa nake kira ga masu ruwa da tsaki da su dauki mataki, baya ga hukunta masu laifin idan an kama su, ina so gwamnati ta bawa mata damar mallakar bindiga da barkonon tsohuwa domin kare kansu daga masu kai musu irin wannan hari domin yi musu fyade.

“An yiwa mata da yawa fyade tare da kashe su. Na tabbata idan aka halattawa mata mallakar wadannan abubuwa za a samu raguwar fyade.

“Baya ga haka, dokar da kasa ta tanada ga masu laifin dokace ta tsawon lokaci, wannan kuwa sha yanzu magani yanzu ce idan har suka samu damar mallakar wadannan abubuwa.

“A kasar Afrika ta Kudu har darasi ake dorawa mata akan yadda ake amfani da wadannan abubuwa don kare kansu a irin wannan yanayi.

Da yake tir da yawaitar fyade a Najeriya, Oluwo ya ce babu wata mace da ta cancanci ayi mata fyade.

Ya ce: “Masu yin fyade ba mutane bane dabobbi ne, halin da mutanen da aka yiwa fyade suke shiga ba abu bane mai dadin ji da ake samo masa magani.

“Wadanda aka yiwa fyade su daina jin kunya ko tsoro. Ku fito kuyi magana sai a taimaka muku. Ba wai shine karshen rayuwa ba. Idan kuka fito kuka bayyana da yawa daga cikin mata za su koyi yadda za su kare kansu daga irin wannan hali da kuka shiga.

“Hatta mata da miji sai sun fuskanci juna kafin su fara yin jima’i. Babu wata mace da ta cancanci ayi mata fyade.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here