A fara gyara a Najeriya ko kuma ta durkushe – Obasanjo yayi gargadi

0
375

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce idan har ba a gyara tsarin gwamnatin tarayya ba, Najeriya za ta cigaba da zama cikin tashin hankali da rashin cigaba.

Obasanjo ya ce matsalolin tsaro sun yiwa gwamnatin tarayya yawa, shine yasa take mantawa da ayyuka masu muhimmanci.

Tsohon shugaban kasar yayi magana ne a jiya Juma’a, a garin Abeokuta na jihar Ogun, a taron da aka saba gabatarwa na shekara-shekara na Sobo Sowemimo.

Taron wanda aka sanyawa suna “Cutar COVID-19 da matsalolin tsaro na Najeriya: mafita”, wata kungiya ce a Abeokuta ta hada taron.

Tsohon shugaban kasar ya zargi gwamnatoci na dukkan matakai da rashin inganci, inda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen nuna damuwarsu kan matsalar tsaro.

Obasanjo ya ce babu lokaci da zamu tsaya mu dinga kallo ko kuma mu cigaba da jira gwamnatin da ba ta da wani inganci ta zo ta kawo mana gyara.

“Ku zo mu dauki mataki da zasu sanya gwamnati dole ta shiga ciki wadanda za su kawo gyara a fannin tsaro, ayyukan yi da tsari.

“A yanda lamura ke tafiya a Najeriya, gaskiya ba ita ce amsa ba, haka kuma hargitsewa da rarrabuwar kawuna nan ma ba shine mafita ba, yin shiru ya sanya mu cikin wannan hali.

“Mafita ta ta’allaka ne akan maza da mata masu karfin hali, kishin kasa, jajircewa, hangen nesa da kuma nuna kauna a lokacin da matsala tayi yawa, da za su jagoranci hanyar samar da sabuwar Najeriya.

“Mu tashi tsaye, da kuma gabatar da kungiya mai taken “Security Matters To All: No Security, No Nigeria”. Lokaci yayi yanzu. “Jinkiri na iya sanya mu cikin wani hali.

“Rashin daukar mataki a yanzu ka iya haifar da karin takaici, tashin hankali da ka iya haifar da komai ya rushe.

“Allah ya kiyaye hakan, “amma ya kamata mu sani cewa hakurin Allah yana da iyaka. Saboda haka dole mu dakata da tunzura shi.

“Allah ya taimaki Najeriya, wacce take daya daga cikin abubuwan da ya kirkira, ya kuma yalwaceta da abubuwa masu albarka.

“Ba zamu dora laifin komai akan Allah ba, saboda yayi iya yin shi, ya kula damu yadda ya kamata, saboda haka abinda ke faruwa damu a yanzu mu muka jawowa kanmu, saboda haka dole mu dora laifin a kanmu.”

Da yake magana game da annobar COVID-19, tsohon shugaban kasar yayi kira da a samar da isashen abinci, tsaro, ayyukan yi da kuma tattalin arziki.

‘Na biyu shine aikin yi da samar da tsaro.

“Na uku a canja tsarin rayuwa ciki kuwa hadda tafiye-tafiye.

“Na hudu shine cigaba a fannin kimiyya, fasaha, kirkire-kirkire da sauransu.

“Abu na biyar shine, sarrafa abubuwan cikin gida.

“Na shida shine habaka tattalin arzikin kasa da kuma habaka kayan masarufi.

“Ya rage namu mu dauki wadannan abubuwa guda shida da muhimmanci.

‘Tare da kyakkyawan shugabanci da manufa mai kyau, tare da kuma hadin kai wajen aiki tare, duka wadannan abubuwa guda shida za a iya kula da su, kuma a kawo karshen matsalar annobar da kuma ciyar da kasar gaba.

“Ina fatan nahiyar Afrika, za ta fito daga matsalar tattalin arziki a wannan lokaci na COVID-19.

“Gare mu ‘yan Najeriya bamu da wata hanya da ta wuce muyi abinda ya kamata.

“Idan ba haka ba, nan gaba abubuwan sai sunfi haka lalacewa, wannan gaskiya ce,” ya ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here