2023: Wata kungiya ta nemi Osinbajo da Zulum su fito takarar shugaban kasa

0
338

Wata kungiya mai suna ‘Good News Nigeria’ ta bukaci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Juma’a 3 ga watan Yuli, ta ce fitowa takarar shugaban kasa ga Yemi Osinabjo da kuma gwamnan Borno, Babagana Zulum a matsayin mataimakin shugaban kasa a 2023 zai taimaka wajen kawo cigaban kasa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A cewar babban jami’in kungiyar, Dauda Mbaya, Najeriya za ta zama daya daga cikin kasashen da za su zama masu cigaba idan aka zabi nagartattun shugabanni a 2023.

Kungiyar ta ce Osinbajo/Zulum a 2023 za su zama sanadiyyar samun cigaban Najeriya.

A bangare daya kuma, kungiyar Miyetti Allah ta ce Tinubu da ‘yan kabilar Igbo ba za su mulki Najeriya a shekarar 2023 ba.

Ya bayyana cewa abinda ake yiwa Hausawa ‘yan Arewa a yankin kudancin Najeriya ba abu bane da zai saka a yadda da su a matsayin shugabanni.

Tinubu da kabilar Igbo ba za su taba mulkar Najeriya ba – Kungiyar Miyetti Allah

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here